Akwai gwamnonin jam’iyyar APC da dama da ke marawa hadakar jam’iyyun adawa ADC baya cikin rudu – Babachir Lawal

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce akwai gwamnonin jam’iyyar APC da dama da ke marawa hadakar jam’iyyun adawa karkashin ADC baya cikin rudu.

A wata hira da gidan talabijin, ya ce tsoron ramuwar gayya ne ke hana su bayyana ra’ayinsu a fili.

Lawal ya ce hadakar na da karfi matuka, kuma tana shirin kalubalantar APC a zaben 2027.

Ya bukaci sauran masu ra’ayi daya da su fito karara su bayyana matsayinsu kamar yadda ya yi.

Kalaman nasa sun tayar da cece-kuce a cikin jam’iyyar APC, inda wasu ke tunanin cewa ya fadi gaskiyar da ke cikin gida.

Comments (0)
Add Comment