Amurka Ta Tabbatar da Turo Dakarunta Zuwa Najeriya Domin Yaƙi da Ta’addanci

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da turo rukunin dakarunta zuwa Najeriya, wannan shine karon farko da Amurka ta amince a hukumance da kasancewar sojojinta a ƙasar tun bayan hare-haren sama da ta kai a watan Disambar da ya gabata.

A cewar rahoton Reuters, shugaban rundunar sojin Amurka a Afirka (AFRICOM), Janar Dagvin Anderson, ya sanar da hakan a ranar Talata, inda ya ce an cimma matsaya tsakanin gwamnatocin Amurka da Najeriya domin ƙara ƙarfafa yaƙi da barazanar ta’addanci a yankin.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ne ya bayar da umarnin kai hare-haren sama kan abin da ya bayyana a matsayin sansanonin ƙungiyar Islamic State a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Duk da cewa jami’an Amurka da na Najeriya sun ce hare-haren makaman na ranar 25 ga Disamba 2025 sun yi nasara, an gano wasu abubuwan fashewa da ba su fashe ba a wuraren da fararen hula ke zaune a jihohin Kwara, Niger da Sokoto.

 Wadannan hare-hare sun zo ne makwanni kaɗan bayan Shugaba Trump ya yi barazanar kai farmaki mai kan Najeriya, bisa zargin “kisan Kiristoci”, zargin da gwamnatin Najeriya ta musanta.

 Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa ‘yan Najeriya na dukkan addinai ne ke fuskantar ta’addancin ‘yan bindiga, tare da roƙon Amurka ta mayar da hankali wajen rushe hanyoyin ta’addanci maimakon yada labaran da ka iya ƙara rarrabuwar kai.

Rahotanni na nuna cewa Amurka na ci gaba da sa ido kan Najeriya ta hanyar jiragen leƙen asiri daga kasar Ghana, a daidai lokacin da Boko Haram da ISWAP ke ƙara faɗaɗa hare-harensu a sassa daban-daban na ƙasar.

Comments (0)
Add Comment