An kama mai safarar bindigogi a tashar mota a Zariya
Dubun wani wanda ake zargi da safarar makamai ta cika, inda aka ƙwato bindigogi ƙirar AK-49 guda biyu, alburusai da wasu kayayyakin laifi a hannunsa a Tashar Motar ’Yan Ƙarfe da ke Sabon Gari a Zariya, a Jihar Kaduna.
’Yan sandan sun gano bindigogi ƙirar AK-49 da kuma daruruwan harsasai iri-iri da miyagun ƙwayoyi a cikin wani buhu da yake ɗauke da shi, wanda ya yi iƙirarin cewa dankali ne a ciki
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai.
Muhammad ya ce an cafke wanda ake zargin mai suna Kenneth, mai shekaru 39, dan asalin Jihar Delta ne, a ranar Talata 25 ga watan Agusta, bayan ’yan sanda sun samu kiran gaggawa cewa ana zargin sa da yin wani abin shakku yayin da yake fama da wata buhu da aka ce dankali ne a ciki.
Ya ce jami’an ’yan sanda daga Sashen Sabon Gari sun kai ɗauki, inda bayan sun binciki buhun suka gano bindigogin AK-49 guda biyu, harsasan RPG guda 228, harsasan AK-47 masu girman 7.62mm guda 275, majalisar AK-47 guda biyar da wasu abubuwan da ake zargin ƙwayoyi ne.
Kwamishinan ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.
A wani samame daban, jami’an Sashen Yaƙi da Satar Mutane na Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar sun cafke wasu mutum uku da ake zargi mambobin kungiyar ’yan bindiga ne a kan Titin Abuja zuwa Kaduna.
Wadanda aka kama sun haɗa da Ibrahim Muhammad mai shekaru 25, Usman Tukur mai shekaru 27 da Hassan Alhaji Salisu mai shekaru 23.
An ce an cafke su ne a ranar 24 ga watan Agusta a yankin Audu Jangwam bayan samun sahihan bayanan sirri.
A cewar kwamishinan, waɗanda ake zargin sun amsa cewa su mambobin wata kungiyar masu ’yan bindiga ne da ke gudanar da ayyukansu a yankin Millennium City da wasu sassan Jihar Kaduna.
Rundunar ta kuma ce ta kwato harsasan AK-47 masu rai guda 134 daga hannun wani mahayi babur da aka tare a kan Titin Kachia a ranar 25 ga watan Agusta.
Muhammad ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Yellow Mai-million ne ya aike shi domin karɓo harsasan tare da kai su wani wuri.
Har ila yau, rundunar ta ce ta cafke wani mutum mai suna Gideon Martins da ake zargi da mallakar makamai a unguwar Sabon Tasha da ke Kaduna.
An ce jami’ai sun kwato wata bindiga ƙirar gargajiya mai harsashi biyu, mari, harsasai masu rai, albarusai, na’urar POS, da wasu kayan jami’an tsaro.
A wani lamari kuma, ’yan sanda sun ce sun gano buhunan ganyayyaki busassu guda 11 da ake zargin tabar wiwi ce a kan Titin Zariya zuwa Kano.
An ce masu wata mota ƙirar Volkswagen Golf Station Wagon wadda ba ta da lambar rajista ne suka gudu suka bar motar da kayan bayan jami’an tsaro suka yi musu kawanya.
A halin da ake ciki, rundunar ’yan sanda tare da haɗin gwiwar Sashen Tsaro na Jami’ar Ahmadu Bello da Civilian Joint Task Force, sun cafke wasu mutum uku kan zargin aikata fashi da makami da kuma fyade a wasu ƙauyukan da ke kusa da Rafin Tukurwa, bayan Jami’ar ABU da ke Zariya.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Jamilu Yau, wanda aka fi sani da Jagwa mai shekaru 20; Abdullahi Hamisu mai laƙabin Maikudi Santsi mai shekaru 25; da Sani Abubakar wanda aka fi sani da Gaye mai shekaru 20.
Kwamishinan ya ce biyu daga cikinsu sun amsa hannu a wasu hare-hare da aka kai a kauyukan Gidan Ƙira, Magata da Gidan Maranta, inda ake zargin su da yi wa mutane fashi da makami tare da lalata mata.
Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun ce suna amfani da wani tsafi da suka kira “sandar kabari”, wanda ake zargin ɗaya daga cikin abokan aikinsu ne ke samar musu da shi.
’Yan sanda sun kuma ce sun cafke wani mutum mai shekaru 27, mai suna Barnabas Amale, kan zargin yunƙurin satar waya da kuma mallakar bindiga a yankin Idon-Gida da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru.
A cewar rundunar, ana zargin mutumin da yi wa wasu mutane barazanar harbe su bayan sun bi shi sakamakon zargin sa da satar wayar hannu.
Rundunar ta ce akwai wani mutum da ake nema dangane da batun bindigar, yayin da wani mutum na uku da ake zargin shi ne ya samar da makamin na ci gaba da gudu.
A wani labari daban, ’yan sanda sun gano wata mota ƙirar Toyota Hilux mallakin Hukumar Samar da Ruwa ta Jihar Kaduna, wadda aka sace daga yankin Unguwar Rimi da ke Kaduna.
Muhammad, ya ce jami’an bincike sun bi sawun motar har zuwa Jihar Kano, inda aka ce mambobin ƙungiyar da ake zargi da satar motar suka gudu suka bar ta bayan an bi su.
Har ila yau, rundunar ta ce ta cafke wasu mutum biyu kan zargin fashi da makami da kuma lalata wasu muhimman kayan gwamnati a Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa da ke Mando a Kaduna.
Ana zargin mutanen da tsallaka katangar cibiyar, tare da daure masu gadi guda biyar kafin su lalata wani na’urar wutar lantarki ta transfoma mallakin cibiyar.
Kwamishinan ’yan sandan ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake kaiwa muhimman kadarorin gwamnati, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar ɓarna ga lafiyar jama’a da tsaron al’umma.
Ya ce rundunar ta ƙara kaimi wajen tattara bayanan sirri, sintiri, kai samame da sauran ayyukan da suka shafi yaki da satar mutane, ’yan bindiga, fashi da makami, satar motoci da sauran laifuka a faɗin jihar.
Muhammad ya buƙaci al’ummar jihar su kasance masu sanya ido tare da kare kadarorin gwamnati da ke yankunansu, sannan su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.
Ya kuma yi kira ga ɓangaren shari’a da su taimaka wajen ba wa ’yan sanda damar gabatar da waɗanda ake zargi a gaban jama’a, musamman waɗanda aka kama da hannu wajen aikata laifi ko kuma aka samu da wasu kayayyakin da ke da alaƙa da laifi.
Ya ce hakan na iya taimakawa wajen ƙara faɗakar da al’umma da kuma sa mutane su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a muhallansu.
Kwamishinan ya yaba wa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Ya tabbatar wa al’ummar Jihar Kaduna cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro da jama’a domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.