’Yan bindiga sun kashe malami, sun sace mutum 10 a Sakkwato
’Yan bindiga sun kashe wani malamin addini bayan sun yi garkuwa da wasu mutane 10 a ƙauyen Gidan Kare a Ƙaramar Hukumar Tureta ta Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin garin ya shaida manema labarai cewa maharan sun kawo harin ne a safiyar ranar Alhamis inda suka tare mutane da ke dawowa daga garin Tureta, inda suke zuwa su kwana, kafin su dawo garinsu da safe domin kauce wa harin ‘yan bindigar a cikin dare.
Majiyar ta ce maharan sun buɗe wuta ga mutane inda suka kashe mutum guda suka yi garkuwa da wasu sama da 10.
“Mutane sukan kwana a garin Tureta domin guje wa harin ’yan bindiga, da safe a dawo gari kowa ya je gidansa, a haka muke tsawon lokaci kafin a kawo mana harin da ba mu zata ba,” in ji shi.
Ya ce, “mutanen da aka yi garkuwa da su sun haɗa da Malam Ɗan Manga, Shehu da Hassan da Hussaini, Badaru da wasu yara biyu diyan Malam Ayuba, Saratu da wasu mutum biyu. Malam Dan Abu ya samu rauni a harin.
“An yi jana’iza ga waɗanda suka rasa ransu, da yawan mutane ba a gansu ba sun bace tun baya kawo harin da aka yi.”
Wakilinmu ya tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ’yan sanda a Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, kan lamarin, amma jami’in ya ce zai bincika daga babban jami’insu da ke Tureta domin samun bayani, amma har zuwa hada rahoton ba a ji daga wurinsa ba.