Atiku Ya Yi Alkawarin Sake Buɗe Iyakokin Najeriya Idan Ya Lashe Zaɓe

Atiku ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin Najeriya idan ya lashe zaɓe

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin Najeriya da ƙasashen makwabta idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027.

Atiku ya ce buɗe iyakokin zai farfaɗo da cinikayyar ƙetare iyaka, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma inganta tsaro ta hanyar dawo da sana’o’in da aka dakatar sakamakon takaita zirga-zirgar kan iyakoki.

Ya ce jihohin Arewa na da iyaka da Nijar, Chadi, Kamaru da Benin, kuma rufe iyakokin ya jefa matasa da dama da ke harkar kasuwanci cikin rashin aikin yi.

Ya kuma yi alkawarin inganta tashoshin jiragen ruwa a Kudu da Kudu maso Gabas domin rage lokaci da kuɗin jigilar kaya zuwa Arewa.

Atiku ya ce hakan zai taimaka wajen daidaita harkokin shigo da kaya da rarraba su a faɗin ƙasar.

Comments (0)
Add Comment