Tinubu Ya Ba da Umarnin Kara Tashoshin CNG 500 Don Rage Kuɗin Sufuri

Tinubu ya ba da umarnin ƙara tashoshin CNG 500 don rage kuɗin sufuri

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba da umarnin kafa wasu ƙarin tashoshin gas na CNG guda 500 a faɗin ƙasar, wanda hakan ya kawo adadin tashoshin da ake shirin kafawa ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na CNG zuwa 1,000.

Tinubu ya bayyana hakan ne biyo bayan tattaunawar da suka yi a taron ƙungiyar Gwamnoni a ranar Alhamis.

Da yake tsokaci kan taron a wata sanarwa da ya sanya hannu da kansa kuma aka wallafa a shafinsa na ɗ a ranar Alhamis, Shugaban ya ce gwamnonin “sun yanke shawara daga gare su, su kaɗai, don ɗaukar matakan gaggawa na rage kuɗin sufuri a jihohinsu, tare da maida hankali kan cin gajiyar fa’idodin arha na CNG da motocin lantarki.”

Ya ce, gwamnatin tarayya ta riga ta zuba jari sosai a fannin sauya fasalin makamashi, inda ya lura cewa ana ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa cibiyoyin sauya fasali da ababen more rayuwa na iskar gas a faɗin ƙasar.

“Gwamnatin Tarayya ta riga ta zuba jari sosai a wannan sauyi na makamashi. Ta hanyar shirin gas ɗin CNG na Shugaban ƙasa, an riga an sauya fasalin motoci sama da 120,000 a faɗin ƙasar, tare da ƙarin kayan sauya fasali fiye da 100,000 da ake kan aiwatarwa. A lokaci guda kuma, muna ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin sauya fasali da ababen more rayuwa na tashoshi a faɗin ƙasar,” in ji Tinubu.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Asusun Kula da albarkatun Gas, na ɗaukar nauyin harkokin aiwatar da gas sama da 100 a faɗin ƙasar, ciki har da manyan tashoshin CNG 15 da ƙananan tashoshi 86.

Tinubu ya ce an ƙaddamar da huɗu daga cikin waɗannan ayyuka a watan Mayu a Legas, Abuja, da Owerri, ciki har da cibiyar tashoshi 15 a Legas da wata cibiya a Abuja da za ta iya hidimtawa motoci da Keken-NAPEP 1,000 da kuma manyan motoci da motocin bus 50 kullum.

Ya ƙara da cewa, “Na kuma ba da umarnin ƙarin kafa wasu sabbin tashoshin gas na CNG guda 500 a faɗin ƙasar, baya ga tashoshi 500 da Asusun ya ba da umarnin kafawa a farkon wannan shekara, wanda hakan zai kawo shirin zuwa tashoshi 1,000 a faɗin ƙasar.”

Tinubu ya ce, wannan faɗaɗawa yana da matuƙar muhimmanci ga sufurin cikin jihohi, inda ya ce ’yan Najeriya ke jin raɗaɗin tsadar kuɗin sosai kai tsaye.

“Abin ya faranta min rai cewa, gwamnoninmu na ɗaukar matakai don kawo waɗannan fa’idodi kusa da mutanen da suke yi wa hidima,” in ji shi.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya da ta jihohi sun amince su kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa don fara aiwatar da matakan rage tsadar kuɗin sufuri nan take.

Ya ce: “Motar da ke amfani da CNG tana kashe kuɗi kusan kashi 60 zuwa 80 cikin 100 ƙasa da wadda ke amfani da man fetur wurin sayen mai.”

Comments (0)
Add Comment