Kwamishinan Hisbah Ya Tilasta Min Saki, Ya Aure Tsohuwar Matata — Magidanci

Kwamishinan Hisbah ya tilasta min saki, ya aure tsohuwar matata — Magidanci

Wani magidanci ya zargi Kwamishina na dindindin na Hukumar Hisbah ta Jihar Zamfara, Faruk Dandalin Faila Kaura Namoda, da aure tsohuwar matarsa, bayan da jami’in ya yi amfani da matsayinsa wajen tilasta raba auren.

Magidancin yana zargin Faruk Dandalin Faila Kaura Namoda, wanda shi ne shugaban kwamitin sulhunta rikicin auren da yin amfani da matsayinsa tare da wani mai suna Sirajo Kwaren Ganuwa, wajen tilasta kashe auren da kuma aure tsohuwar matar tasa mai suna Aisha.

Ya bayyana hakan ne a cikin takardar koken da ya aike wa Gwamnatin Jihar Zamfara takardan koke, inda ya zargi wani Kwamishinan Hisban da din wani mai suna Sirajo Kwaren Ganuwa da yin amfani da matsayinsu wajen tsoma baki a rigimar aurensa.

A cikin takardar koken mai dauke da kwanan wata 26 ga Agusta, 2026, wadda aka miƙa wa Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara (SSG), mutumin ya ambaci Faruk Dandalin Faila Kaura Namoda, wanda ya bayyana a matsayin mamba na dindindin a Hukumar Hisbah ta jihar, da kuma Sirajo Kwaren Ganuwa, da cewa a kansu kaɗai yake ƙorafi, ba a kan Hukumar Hisbah ta Jihar Zamfara ba.

Ya buƙaci gwamnatin jihar ta gudanar da bincike mai zaman kansa domin gano halin da ake ciki da kuma irin rawar da mutanen biyu suka taka wajen rikicin aurensa.

A cewarsa, matsalar ta samo asali ne daga rashin jituwa tsakaninsa da tsohuwar matarsa mai suna Aisha, inda ya ce an yi ƙoƙarin sasanta tsakaninsu sai dai ba a yi nasarar sulhunta su ba.

Ya yi zargin cewa shiga tsakani da Sirajo Kwaren Ganuwa da Faruk Dandalin Faila suka yi ya wuce gona da iri, inda ya ce an yi amfani da matsin lamba da tasiri wanda daga baya ya kai ga wargajewar aurensa.

Mai ƙarar ya kuma yi zargin cewa Faruk Dandalin Faila, wanda ya ce shi ne shugaban kwamitin da ya jagoranci sasancin rikicin aurensu, daga baya ya auri Aisha bayan abin da ya bayyana a matsayin matsin lamba da ya tilasta a raba aurensu.

Saboda haka, ya roƙi gwamnatin jihar da ta binciki yadda kwamitin ya gudanar da lamarin tare da gano ko wani daga cikin waɗanda suka shiga tsakani ya wuce iyakar ikonsa.

Ya kuma buƙaci a bincika ko Sirajo Kwaren Ganuwa da Faruk Dandalin Faila sun shiga lamarin ne a matsayinsu na kashin kansu ko kuma sun yi amfani da muƙamansu, tasirin hukumominsu ko kuma irin ƙarfin da ake ganin suna da shi a matsayin jami’an gwamnati.

Wani muhimmin ɓangare na ƙorafin ya shafi batun kula da ’ya’yan mai ƙarar guda biyu. Ya yi zargin cewa a halin yanzu ’ya’yan suna ƙarƙashin kulawar Sirajo Kwaren Ganuwa, inda ya nemi a binciki yadda suka shiga hannunsa.

Mai ƙarar, wanda ya bayyana kansa a matsayin mahaifin yaran na jini, ya roƙi gwamnati ta binciki lokacin da yaran suka shiga hannun Ganuwa da kuma ko akwai wata kotu da ta bayar da umarni, yarjejeniya ta doka ko wata hujja ta shari’a da ta ba shi damar riƙe yaran.

Ya kuma nemi a binciki inda yaran suke yanzu, yanayin rayuwarsu da kuma wanda ke kula da bukatunsu na yau da kullum.

A cewarsa, ya kamata a tabbatar da lafiyar yaran, karatunsu, tsaronsu da kuma walwalar tunaninsu, ba tare da la’akari da yadda rikicin aurensu ya kasance ba.

Ya kuma yi zargin cewa ana iya samun amfani da matsayi, tsoratarwa ko matsin lamba wajen batun kula da yaran, inda ya nemi hukumomi su gano gaskiyar lamarin.

Mai ƙarar ya ce babban abin da yake damun sa shi ne tabbatar da cewa ba a raba shi da ’ya’yansa ba tare da ingantacciyar hujjar doka ba.

Ya kuma roƙi gwamnati ta binciki yadda aka yi aure tsakanin Faruk Dandalin Faila da tsohuwar matarsa, musamman dangane da ko an samu wani amfani da matsayi, rashin da’a a wajen aiki ko kuma tsoma baki ba bisa ƙa’ida ba.

Da aka tuntubi Sirajo Kwaren Ganuwa, ya musanta zarge-zargen da aka yi masa, inda ya ce yana da kyakkyawar alaƙa da mai ƙarar, kuma an bi hanyoyin da suka dace wajen gudanar da batun rikicin auren.

Ganuwa ya ce ya shiga lamarin ne a matsayinsa na babban ɗan uwa ga Aisha, inda ya ce a lokuta da dama ya ƙarfafa mata gwiwa ta koma gidan mijinta duk da cewa ba ta son komawa.

“Ni a matsayina na babban ɗan uwa ga Aisha, na tilasta mata ta koma gidan mijinta a lokuta da dama, duk da cewa ba ta so kuma tana da ƙorafe-ƙorafe da dalilai masu ƙarfi,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa zarge-zargen da ake yi masa ba su da tushe, yana mai cewa an bi hanyoyin da suka dace wajen sasanta lamarin.

Game da rikicin mallakar ’ya’yan kuwa, Sirajo ya ce bai taɓa hana wa mahaifin yaran daukarsu na wani ɗan lokaci ba, sai dai ba za su amince ya ɗauki yaran ba domin a halin yanzu ba shi da aure.

“Domin tabbatar da kare lafiya da tarbiyar yaran ba za mu amince ya ɗauke su na dindin ba, domin ba shi da aure balantana ya kula da su yadda ya dace.

“Sai da na sanya yaran wata babbar makarantar da yarana ke karatu da Islamiyya amma ya ƙeƙashe ƙasa ya ce sai ya canza musu makaranta na kuma amince duk da makarantar da ya kai su ba ta da inganci,” in ji Sirajo.

Duk Ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Zamfara, Malam Umar Hassan Gusau, bai yi nasara ba.

Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, bai mayar da martani ga kiran waya, saƙonnin SMS da WhatsApp da aka aika masa domin jin ta bakinsa kan zarge-zargen ba.

‘Ina da hujjoji idan ana buƙata’

Mai ƙarar ya ce yana da shirin gabatar da takardu, saƙonni da sauran hujjojin da ke hannunsa domin taimaka wa duk wani bincike da hukumomi za su gudanar.

Ya kuma roƙi a ba shi kariya da kuma kiyaye sirrinsa saboda tsoron yiwuwar ramuwar gayya ko tsoratarwa sakamakon shigar da ƙorafin.

Daga cikin buƙatunsa, ya nemi SSG ya tabbatar da karɓar ƙorafin, ya miƙa zarge-zargen da ake yi wa Ganuwa ga hukumar da ta dace domin bincike, sannan ya miƙa zarge-zargen da ake yi wa jami’in Hisbah ga hukumar da ta dace.

Ya kuma buƙaci a ɗauki matakin da ya dace idan bincike ya tabbatar da an samu laifi ko rashin da’a.

Mai ƙarar ya ce ya shigar da ƙorafin ne da kyakkyawar niyya, ba da nufin ɓata suna ko yi wa wani daga cikin mutanen da aka ambata ƙarya ba, sai dai domin neman adalci da kuma shiga tsakani na hukumomi ba tare da son rai ba.

Comments (0)
Add Comment