Ya kamata a kyautata rayuwar talaka bayan cire tallafin mai – Atiku
Kusan mako biyu ke nan ana ta ce-ce-ku-ce tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana aniyarsa ta cire tallafin man fetur idan ya hau kan mulki a 2027.
Kamar mutane da dama a Najeriya, Atiku na ganin cewa cire tallafin man fetur shi ne silar matsalolin matsin tattalin arziƙi da al’ummar ƙasar ke ciki.
“Ana cikin ƙunci, ana cikin rashi da rashin aikin yi, wannan tallafin man fetur da aka janye shi ne babban abin da ya haifar da hakan. Ban taɓa ganin an sha wahala ba a ƙasar nan kamar wannan lokaci,” in ji Atiku a tattaunawar da BBC.
Gwamnatin Najeriya ta mayar wa Atiku martani, inda ta bayyana cewa batun tamkar rashin fahimtar abin da ke faruwa ne da tattalin arziƙin ƙasar.
Sai dai a tattaunawar da BBC, Atiku ya ce cire tallafin man fetur da zai yi ya dogara ne da halin da ya tsinci ƙasar idan ya kama mulki.
Atiku ya ce: “Ko za ka cire tallafin man fetur, ba a lokaci ɗaya za ka yi shi ba , kuma sai ka kyautata rayuwar talakawa kafin ka fara cirewa a hankali”.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ƙasar.
Lamarin ya haifar da tashin farashin man fetur nan take, wani abu da ya shafi dukkanin fannonin rayuwa na al’ummar ƙasar.
Haka nan Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, wanda duk ake alaƙantawa da cire tallafin na man fetur.
Tun farko gwamnatin Tinubu ta yi alƙawarin samar da shirye-shirye da za su sauƙaƙa wa al’ummar ƙasar tsananin rayuwa, to amma sama da shekara uku bayan cire tallafin al’umma da dama a ƙasar na cewa ba su ga wannan tallafi ba.
Ministan Kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele ya ce an tara jimillar naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen tallafin man fetur ɗin tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.
Ministan ya ce gwamnatin ta kashe kuɗaden ne ta hanyar raba wa jihohi da yin ƙarin albashi da alwus ɗin ma’aikata da biyan basukan da ake bin ƙasar da kuma gudanar da manyan ayyuka.