An Kashe Mutum 20 A Sabon Hari A Filato

An kashe mutum 20 a sabon hari a Filato

Mutane aƙalla 20 ne ake zargin an kashe su a wani sabon hari a yankin Binkyap da ke Shiyyar Bai a Ƙaramar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato.

An kai sabon harin ne ƙasa da mako guda bayan wani da aka kashe wasu mutum uku, inda kabilun Mwaghavul da Fulani suke zargin juna da kashe-kashe da kuma ƙone-ƙone.

Shugaban Ƙungiyar Ci-gaban Al’ummar Mwaghavul, Bulus Dabit, ya ce annkai harin ne a cikin tsakar dare a yayin da jama’a suke barci.

Wani ganau, Daniel Musa, ya shaida wa wakilinmu cewa maharan suna ɗauke ne da manyan makamai inda suka riƙa shiga gidaje suna kai wa iyalai hari.

Ya ce, “Kafin wayewar garin yau Talata wasu mahara ɗauke da muggan makamai suka kawo mana hari. Sun riƙa shiga gida-gida suna buɗe ƙofofin suna kashe mutane a yayin da suke barci a cikin gidajen.

“Zuwa safiyar nan mun tabbatar da mutuwar mutane 20, baya da wasu da dama da da aka jikkata da kuma wafanda suka ɓace,” in ji shi.

Comments (0)
Add Comment