An Tsare Mai Satar Takalma A Masallacin Kotu A Kano

An tsare mai satar takalma a masallacin kotu a Kano

Wata Kotun Majistare mai lamba 53 da ke zaune a Norman’s Land a Kano ta bayar da umarnin tsare wani mutum, Muhammad Najib Rimin Kebe, a gidan gyaran hali kan zargin yawan sace-sacen takalman jama’a a masallacin da ke cikin harabar Kotun.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan sanda ne suka gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotun da Mai Shari’a Dayyabu Jamilu Hamza ke jagoranta, bisa tuhume-tuhumen da suka shafi kutsen ba bisa ƙa’ida ba da kuma satar takalma a masallacin.

Kotun ta umarci Adam Salisu Tarauni da ya karanta wa wanda ake tuhuma tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali, sannan ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Agusta, 2026.

Tun farko dai ana zargin wanda ake tuhuma da yawan zuwa masallacin da ke cikin harabar kotunan yana wawushe takalman jama’a.

Wasu daga cikin waɗanda suka shigar da ƙorafi, ciki har da ma’aikatan kotu, jami’an ’yan sanda, ma’aikatan hukumar gyaran hali da sauran jama’a, sun ce an daɗe ana fuskantar matsalar satar takalma a masallacin.

Comments (0)
Add Comment