Dan Sanda Ya Harbi Dan Kasuwa A Shingen Bincike A Filato

Dan sanda ya harbi ɗan kasuwa a shingen bincike a Filato

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta tsare wani jami’inta da ake zargi da harbin wani ɗan kasuwa a wani shingen bincike da ke Ƙaramar Hukumar Riyom ta jihar.

Dan sandan ya harbi mutumin a kafa ne a ranar 11 ga watan Agusta, lokacin da aka tsayar da ɗan kasuwar mai suna Danladi a wani shingen bincike, yayin da yake safarar kayan lambu zuwa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Kakakin rundunar, SP Alfred Alabo, ya tabbatar da kama jami’in a ranar Lahadi, inda ya ce an ƙwace bindigarsa tare da kulle shi domin ci gaba da bincike.

Ya ce, “Bayan samun labarin lamarin, nan take DPO na Riyom da jami’ansa ya je wurin, ya kwace wa jami’in makami sannan ya kai shi sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), inda ake yi masa tambayoyi tare da ladabtarwa,” in ji Alabo.

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya umarci DPO ɗin da ya ziyarci asibitin da ake kula da wanda aka harba domin duba halin da yake ciki tare da gabatar da rahoto kan yanayin lafiyarsa.

Kakakin rundunar ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa yin arangama da jami’an tsaro da ke ɗauke da makamai, yana mai gargadin cewa lamarin yana iya kazancewa.

Ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar na gudanar da bincike kan lamarin, kuma za ta sanar da su duk wani sabon abin da binciken ya gano.

Comments (0)
Add Comment