Darajar Naira ta yi faduwar da ba’a taba ganin irin ta ba tun shekarar 1999

Ta cikin wani dogon jawabi da kididdiga da mujallar tattalin arziki ta Bloomberg ta fitar ta ce shekaru kusan 25 kenan rabon da dala ta tumurmusa Nairar a kasuwar chanji.
Mujallar bata tsaya iya nan ba sai da ta yi hasashen cewa darajar nairar zata ci gaba da faduwa warwars a shekararda 2024, matukar mahukunta basu yi gaggawar daukar mataki ba.
Bayanai na nuna cewa Nairar ta fadi da kaso 55 cikin dari a bana kadai, inda a jiya aka rika sayar da kowacce dalar Amurka daya a kan naira 1,043, abinda ya sanya kudin na Naira ya fadawa cikin jerin kudade marasa daraja a duniya bayan Fan na Lebanon da Peso na Argentina da ke biye mata a baya.
Kididdigar mujallar ta ci gaba da cewa faduwar darajar Nairar ya fara ne tun lokacin da babban bankin kasa CBN ya bar kasuwa ta yi halinta a fannin sauyin kudade, kari akan haka kuma shugaba Tinubu ya cire talllafin man fetur.
Haka kuma mujallar ta ce a yanzu asusun kasashen waje na Najeriya na ganin tasku, kasancewa kullum kasa ya ke yi tun shekaru 6 da suka gabata, abinda ke da nasaba da wasu ka’idojin tattalin arziki da kasashen turai ke kakabawa Najeriya da sunan bayar da tallafi.

Comments (0)
Add Comment