Hukumar Sadarwa ta Kasa ta ce kawo yanzu kudaden Rabanu da ta tara ya kai kimanin Naira Biliyan 150

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ce kawo yanzu kudaden Rabanu da ta tara ya kai kimanin Naira Biliyan 150 fiye da abinda tayi hasashen tarawa na Naira Biliyan 36 cikin watanni 5 kadai.

Hukumar NCC ta ce kudaden data tara ya haura kaso 400 na kudaden Rabanu data yi hasashen tarawa daga ranar 1 ga watan Janeru zuwa 31 ga watan Mayu na wannan shekara, wanda hakan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tayi sauye-sauye a fannin.

Haka kuma Hukumar ta ce abinda ta tara yana daga cikin dokokin ayyukan hukumar na shekarar 2003, wanda ya bawa hukumar damar tara kudaden Haraji.

Kazalika hukumar ta ce abinda ta gabatarwa da Majalisar Kasa na abinda zata tara na kudaden Haraji cikin watanni 5 shine Naira Biliyan 36, amma yanzu abin ya sauya da gagarumar nasara.

Comments (0)
Add Comment