Malaman Jami’ar KASU Sama da 200 Sun Bar Aiki — ASUU

Malaman Jami’ar KASU sama da 200 sun bar aiki — ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta ce sama da malamai 200 sun bar jami’ar saboda rashin ingantattun yanayin aiki da kuma rashin fara aiwatar da yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta kulla da ASUU a 2025.

Shugaban ASUU-KASU, Dakta Abubakar Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kaduna ranar Litinin.

Ya ce yarjejeniyar, wadda ta fara aiki tun watan Janairu 2026, har yanzu ba a fara aiwatar da ita a KASU ba, lamarin da ya sanya malaman jami’ar cikin waɗanda ake biyan su albashi mafi ƙaranci a jami’o’in ƙasar nan.

Ƙungiyar ta ba wa mahukuntan jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin makonni biyu su fara aiwatar da yarjejeniyar, ko kuma ta ɗauki matakin yajin aikin gama-gari da ba shi da wa’adi.

ASUU ta ce mafi yawan malaman da suka bar jami’ar sun hada da farfesoshi, mataimakan farfesoshi da masu digirin digirgir, waɗanda suka samu aiki a wasu jami’o’i.

Ta kuma buƙaci a biya malaman bashin albashi da ya taru tun daga watan Janairu 2026 tare da inganta albashi da sauran abubuwan da suka shafi yanayin aiki.

Har yanzu mahukuntan KASU ba su mayar da martani kan zarge-zargen ƙungiyar ba.

Comments (0)
Add Comment