Reshen jihar Jigawa na hukumar jami’an tsaron na Civil Defense yace ya kwato kudi sama da Naira miliyan 9 da dubu 700 na basussuka a jiharnan cikin watanni 6 da suka gabata.
Kakakin rundunar, Adamu Abdullahi, ya sanar da haka cikin wata sanarwa a Dutse.
Adamu Abdullahi yace an karbo kudaden biyo bayan korafe-korafe da hukumar ta karba daga wanda suka bayar da bashin.
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
- Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina
- Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana
- EFCC Ta Gurfanar da Bello Bodejo Kan Zargin Badaƙalar Kuɗi
Yayi bayanin cewa basussukan da aka karbo na daga cikin korafe-korafe 114 na fararen hula da hukumar ta yi aiki akai tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana.
Kakakin yayi nuni da cewa yawan korafe-korafe da basussukan da aka karbo cikin watannin sun ragu sosai idan aka kwatanta da na baya.