Masu Taurin Bashi A Jigawa Sun Amayo Shi Da Taimakon Civil Defence

0 80

Reshen jihar Jigawa na hukumar jami’an tsaron na Civil Defense yace ya kwato kudi sama da Naira miliyan 9 da dubu 700 na basussuka a jiharnan cikin watanni 6 da suka gabata.

Kakakin rundunar, Adamu Abdullahi, ya sanar da haka cikin wata sanarwa a Dutse.

Adamu Abdullahi yace an karbo kudaden biyo bayan korafe-korafe da hukumar ta karba daga wanda suka bayar da bashin.

Yayi bayanin cewa basussukan da aka karbo na daga cikin korafe-korafe 114 na fararen hula da hukumar ta yi aiki akai tsakanin watan Janairu zuwa Yunin bana.

Kakakin yayi nuni da cewa yawan korafe-korafe da basussukan da aka karbo cikin watannin sun ragu sosai idan aka kwatanta da na baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: