Dalilin Da Ya Sanya Ba Za a Sake Bayar Da Belin Wanda Ake Zargi Da Fyade A Kaduna Ba

0 211

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna yace bangaren shari’a a jihar bazai sake bayar da belin masu fyade ba, daidai lokacin da ake duba yiwuwar dandake wadanda aka yankewa hukuncin fyade.

El-Rufa’i ya sanar da haka lokacin da wata tawagar mata da ke neman adalchi ga wadanda ake yiwa fyade, ta shirya wata zanga-zangar lumana a gidan gwamnati dake Kaduna a jiya.

Yace alkalin alakai na jihar ya bayar da tabbacin cewa daga yanzu baza a sake bayar da belin duk wanda aka zarga da aikata fyade ba, ta kowane hali, kasancewar suna komawa su sake aikata laifin.

A cewarsa, tuni jihar take da tsatstsauran hukunci akan laifin aikata fyade.

Sai dai, El-Rufa’i yace gwamnati na duba yiwuwar gyaran dokar domin sanya dandaka ga duk wanda aka zartarwa da hukuncin fyade.

A cewarsa, tuni wani dan majalisar dokokin jihar ya shirya gabatar da kudiri akan sanya dandaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: