Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Everton kuma ɗan asalin ƙasar nan Alex Iwobi ya shiga cikin jerin matasan yan wasan Everton wadanda za,azaɓi daya daga cikin su, domin a bashi kyautar gwarzo matashin ɗan wasan kungiyar na bana.

Wannan sanarwar ta fito ne, ta shafin sada zumunta na kungiyar inda suka bayyana sunayen yan wasan har guda 8 da magoya bayan kungiyar zasu kaɗa kuri,unsu akan wanda suke ganin yafi cancanta ya lashe kyautar ta bana.
Cikin yan wasan da za,azaɓa sun hada da Dominic Calvert-Lewin, Tom Davies, Anthony Gordon, Mason Holgate, Jean-Philippe Gba da dai sauransu.

Iwobi Mai shekara 24 ya koma Everton daga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kakar wasanni ta bara.
Tin bayan zuwan sa kungiyar yake taimaka mata, inda yanzu haka suke a matsayi na 11 a teburin gasar firimiytar kasar ta Ingila da ake shirin kammalawa.

Yanzu haka a tarihi an bayyana cewa akwai yan wasan kasar nan da suka taɓa lashe irin wannan kyautar kamar su Daniel Amokachi, Joseph Yobo,Yakubu Aiyegbeni da kuma Victor Anichebe.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: