Mutumin da ya samar da jaridar Democrat kuma tsohon shugaban kungiyar masu gidajen jarida na kasa, Mallam Ismaila Isa Funtua, ya rasu.
Ya mutu sanadiyyar bugun zuciya jiya Litinin da dare. Marigaryin ya rasu yana da shekaru saba’in da shida a duniya.
Babban mai taimakawa shugaban kasa akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Mallam Garba Shehu, a cikin wata sanarwa yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matsananciyar damuwa da samun labarin mutuwar abokin tafiyarsa a siyasance, Isa Funtua.
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
- Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina
- Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana
- EFCC Ta Gurfanar da Bello Bodejo Kan Zargin Badaƙalar Kuɗi
Ana kyautata zaton cewa Isa Funtua na daya daga cikin masu karfin fada aji a gwamnatin Buhari.
Ance Isa Funtua tare da tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasa Abba Kyari da dan yayan shugaban kasa, Mamma Daura, sune wadanda suka fi kowa karfin iko a gwamnatin Buhari.