Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da nuna ƙauna da biyayya ga ƙasarsu duk da irin ƙalubalen da take fuskanta, musamman matsalar rashin tsaro.
Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, yayin da Najeriya ke cika shekaru 27 tana gudanar da mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.
A cewarsa, duk da nasarorin da aka samu a tafiyar dimokuraɗiyya, akwai abubuwa biyu masu tayar da hankali da suka faru a daidai lokacin bikin, waɗanda suka haɗa da sace ɗaliban makaranta a jihohin Oyo da Borno.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba za ta iya bunƙasa yadda ya kamata ba idan babu tsaro, yana mai jaddada cewa zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma na daga cikin muhimman ginshiƙan mulki nagari.
“Dimokuraɗiyya ba tare da tsaro ba, ba za ta iya samar da cikakken ci gaba da walwalar jama’a ba,” in ji shi.
Tinubu ya ce saboda muhimmancin lamarin, gwamnatin tarayya ta ayyana matsalar tsaro a matsayin abin da ke bukatar matakan gaggawa, inda ta amince da ɗaukar sabbin jami’an ‘yan sanda sama da 50,000, tare da ƙara yawan sojoji da sauran jami’an tsaro domin ƙarfafa yaƙi da masu aikata laifuka.
Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da kayan aiki da dabarun da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.
A ƙarshen jawabinsa, Shugaba Tinubu ya yi jinjina ga marigayi Moshood Kashimawo Olawale Abiola (MKO Abiola), wanda ake tunawa da shi a ranar 12 ga Yuni saboda rawar da ya taka a gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ya ce Abiola ya kasance jagora wanda ya samu karɓuwa daga al’ummu daban-daban ba tare da la’akari da bambancin addini, ƙabila ko al’ada ba, yana mai cewa gudummawarsa za ta ci gaba da zama abin koyi ga masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar ƙasar.