Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana shirinta na tura sama da mambobin NYSC miliyan 1.4 a matsayin ma’aikatan wucin gadi domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin Hukumar Bautar Ƙasa (NYSC) a Abuja, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da ‘yan bautar ƙasa ke takawa wajen gudanar da zaɓe tun bayan dawowar dimokraɗiyya a shekarar 1999.
A cewarsa, za a buƙaci ma’aikatan NYSC 707,384 domin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya, sannan za a sake amfani da adadin makamancin haka wajen gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisun jihohi, wanda ya kai jimillar mutane 1,414,768.
Amupitan ya bayyana cewa ‘yan NYSC su ne ginshiƙin ayyukan zaɓe a Najeriya, musamman a matsayin jami’an rumfunan zaɓe da masu kula da tantance masu kaɗa ƙuri’a, yana mai cewa INEC ba za ta iya gudanar da zaɓe yadda ya kamata ba tare da gudunmawar su ba.
Hukumar ta kuma yi alƙawarin ƙara inganta tsaro, inshora da walwalar mambobin NYSC da za a tura domin ayyukan zaɓe a faɗin ƙasar