Matashi ya kashe mahaifiyarsa da adda a Ondo
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta cafke wani matashi mai shekaru 23, Samuel Akoade, bisa zargin kashe mahaifiyarsa, Misis Olufunke Amoo a garin Ore da ke Ƙaramar Hukumar Odigbo ta jihar.
Aminiya ta ruwaito rundunar ’yan sandan tana bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 16 ga Agusta, 2026.
A cewar ’yan sandan, an tarar da matar mai shekaru 60 kwance jina-jina a gidanta, tana ɗauke da munanan raunuka na saran adda a jikinta.
Rundunar ’yan sandan da ke Ore ta ce jami’anta sun garzaya wurin bayan samun rahoton lamarin, inda suka killace wurin domin fara bincike.
Sanarwar ta ce an gano wata adda da ake zargin da ita aka yi amfani wajen kaiwa matar hari a wurin da lamarin ya faru, yayin da ake zargin wanda ya aikata laifin ya tsere kafin isowar ’yan sanda.
Sai dai jami’an tsaron sun fara farautarsa, kuma daga bisani suka samu nasarar kama Samuel Akoade wanda yanzu haka yana tsare.
“An kai gawar marigayiyar ɗakin ajiye gawarwaki, yayin da wanda ake zargin ke hannun ’yan sanda.
“An mayar da ragamar lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Akure domin ci gaba da bincike,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ondo, CP Felix Ohagwu, ya umarci a gudanar da cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya kai ga kisan tare da tabbatar da an yi wa kowa adalci.
Rundunar ta kuma sake tabbatar wa mazauna jihar aniyarta ta kare rayuka da dukiyoyi, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suke zargi da wuri a yankunansu.