Miji ya banka wa matarsa wuta saboda riga
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta kama wani mutum, Jacob Irewa, bisa zargin banka wa matarsa, Berida Irawo, wuta bayan saboda rigunansa.
An ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da rana a gidansu, sakamakon rashin jituwa da ta taso kan wasu rigunansa masu gajerun hannu da suka ɓace.
Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan Irewa ya gano cewa rigunansa masu gajerun guda bakwai, waɗanda ya ce yana matuƙar so, ba sa cikin ɗakinsa.
A cewar wanda ake zargin, ya dawo gida daga waje, ya yi wanka, sannan ya so ya saka ɗaya daga cikin rigunan, amma bai same su ba.
Ya ce ya bincika ko’ina, ciki har da wurin da suke shanya tufafi bayan ginin.
Ya ce lokacin da ya tambayi matarsa game da rigunan a cikin ɗaki, sai ta gudu zuwa waje, tana gaya masa cewa ta ƙona su, bayan da ya matsa mata da tambayoyi.
Ya ce, “Na tambaye ta dalilin ƙona su. Saboda takaici da fushi, sai na je inda na ajiye babur ɗina, na ɗebo fetur, na watsa mata sannan na kunna mata wuta da ashana.
“Ban san yadda abin ya faru ba. Allah Ya yi mini rahama,” in ji shi.
Wanda ake zargin ya ce shi fasto ne, kuma malamin makaranta ne a ƙauyen Irawo, amma a halin yanzu yana hutu a Lokoja.
Ya kuma yi iƙirarin cewa bai taɓa yin faɗa da matarsa kan wani abu ba, sannan ya ce sun shafe shekaru da aure ba tare da samun ɗa ba.
Rundunar ’Yan Sandan Kogi ta tabbatar da kama shi bisa zargin yunƙurin kashe matarsa, Berida Irawo.
Kakakin rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce an samu rahoton lamarin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare ranar Juma’a, 14 ga Agusta, 2026.
Ta ce binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwar cikin gida, bayan matar ta ƙona wasu tufafin mijinta da take ganin ba ya amfani da su, ba tare da izininsa ba.
“Daga nan wanda ake zargin ya yi mata barazana, ya ɗebo fetur daga babur ɗinsa sannan ya banka mata wuta,” in ji ta.
Kakakin ’yan sandan ya ce matar ta tsira daga harin kuma a halin yanzu tana karɓar magani a asibitin Honey Gold da ke Felele.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amince a bayanansa ga ’yan sanda cewa shi ne ya banka wa matarsa wuta.
A cewarsa, rundunar ta fara cikakken bincike domin gano ainihin abin da ya faru da kuma tattara ƙarin shaidu kan lamarin.