(NRC) Ta Bayyana Cewa An Fara Bincike Kan Hatsarin Jirgin ƙasa Daga Abuja Zuwa Kaduna

Hukumar jiragen ƙasa ta kasa (NRC) ta bayyana cewa an fara bincike kan hatsarin da jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham dake jihar Kaduna.

Hukumar ta ce binciken zai gudana ne ƙarƙashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta Tarayya domin gano musabbabin lamarin.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Talata da yamma, ta bayyana cewa jimillar mutane 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan layi.

Hukumar ta ce daga cikin fasinjojin, mutane bakwai ne suka samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti.

Sauran fasinjojin kuwa an mayar da su zuwa tashoshin Idu da Kubwa ta wani jirgi da aka tura daga Abuja.

An kuma dakatar da dukkan ayyuka da zirga-zirgar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna na ɗan lokaci, har sai an kammala aikin ceto da bincike da kuma gyara wurin.

Comments (0)
Add Comment