PDP na zawarcin Sanata Goje don ya taimaka wa takarar Pantami a Gombe
Ana ci gaba da yi wa tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje matsin lambar ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta PDP domin ya mara wa ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Farfesa Isa Ali Pantami, baya a Zaɓen 2027.
Majiyoyi sun tabbatar wa wakilinmu cewa tsohon Gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, da Pantami na ci gaba da zawarcin Goje, tare da matsa masa lamba ya koma PDP, musamman bayan da aka samu labarin cewa APC ba za ta ba shi tikitin takarar Majalisar Dattawa ba.
Wasu jiga-jigan PDP na ganin cewa komawar Goje tare da ɗinbim magoya bayansa da abokan siyasarsa da ke faɗin mazaɓun sanatoci uku na jihar zuwa PDP, zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi tare da inganta damar Pantami ta lashe zaɓen gwamna.
Goje, wanda ya kasance Sanatan Gombe ta Tsakiya tun 2011 bayan ya kammala wa’adi biyu a matsayin gwamnan jihar, ya fuskanci tangarɗa a ƙoƙarinsa na komawa Majalisar Dattawa a karo na biyar, bayan da bai samu tikitin APC ba a zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.
Kwamitin APC da ke kula da zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar majalisar wakilai da sanatoci a Gombe ya bayyana DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya) a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya.
Sai dai Goje, ta bakin mai taimaka masa na musamman, Ahmed Isa Kashere, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fidda gwanin, yana mai cewa sakamakon da aka sanar ba gaskiya ba ne, inda ya ce za a fitar da sahihin sakamakon a Abuja.
Bayan rashin ganin sunan Goje cikin jerin sunayen ‘yan takarar majalisar tarayya da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fitar a ranar Asabar ɗin da ta gabata, sai aka fara samun rahotannin cewa tsohon gwamnan na duba yiwuwar komawa PDP domin ci gaba da riƙe kujerarsa a majalisar dattawa.
Haka kuma, an ce PDP da ADC na zawarcin Goje, wanda ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin siyasar Gombe, domin ya koma cikinsu da nufin ƙarfafa damar jam’iyyun a zaɓen 2027.
Sai dai wata majiya daga tawagar Goje, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Goje da shugabannin PDP kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar.
Goje wanda yana daya daga cikin waɗanda suka kafa PDP a shekarar 1998, ya taɓa zama Minista na Ma’aikatar Wutar Lantarki da Karafa a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a wa’adinsa na farko.
Daga bisani, ya zama gwamnan Gombe na tsawon wa’adi biyu a ƙarƙashin PDP.
A shekarar 2014, Goje ya koma APC, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa jam’iyyar ƙwace mulki daga hannun PDP a jihar a shekarar 2019.
Sai dai daga baya dangantakar siyasa tsakanin Goje da yaronsa na siyasa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta yi tsami, lamarin da ya kai ga kayar da shi a zaɓen fidda gwani na APC da aka gudanar a watan Mayun da ya gabata.
Batun Pantami
Wakilinmu ya gano cewa tawagar Pantami na ƙoƙarin ganin Goje ya koma PDP, ganin cewa har yanzu ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan siyasar Gombe, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake ciki ba.
Masu goyon bayan Pantami na ganin cewa komawar Goje PDP na iya sauya tsarin ƙawancen siyasa a jihar tare da ƙara wa jam’iyyar hamayya ƙarfi gabanin zaɓen 2027.
Wasu masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce fitowar Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan PDP ta ƙara wa jam’iyyar damar samun nasara a zaɓen.
A halin yanzu, Pantami na da ɗinbim magoya baya, musamman tsakanin matasa da al’ummomin karkara, waɗanda ke kallonsa a matsayin wanda zai kawo sauyi.
Wani mai sharhi kan siyasa, Musa Tijjani, ya ce ya kamata ‘yan jam’iyyar su haɗa kai wajen marawa dukkan ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar baya domin samun kujeru da dama da za su ƙara mata ƙarfi gabanin zaɓen gwamna.
Ya ce: “Tun bayan komawar Pantami PDP, farin jinin jam’iyyar ya ƙaru. Idan Goje ma ya koma PDP, hakan zai kawo babban sauyi a siyasar Gombe.
“Saboda haka, yawancin masu zaɓen da ke goyon bayan tsohon gwamnan za su je rumfunan zaɓe su zaɓi ‘yan takarar jam’iyyar a dukkan matakan zaɓe.
“Har Pantami da kansa zai yi farin ciki idan ya samu mutane irin Sanata Danjuma Goje a cikin jam’iyyar, domin hakan zai ƙara wa magoya bayansa kwarin gwiwa. Goje ma zai iya mayar masa da irin wannan goyon baya a lokacin zaɓen gwamna.”
Masu lura da harkokin siyasar jihar sun bayyana cewa, idan Goje ya koma PDP, hakan na iya sauya tsarin siyasar Gombe tare da haifar da babban ƙalubale ga APC mai mulki a zaɓen 2027.