PDP Ta Buƙaci Bahasi Kan Naɗin Manyan Sakatarori 19 A Gombe

PDP ta buƙaci bahasi kan naɗin manyan sakatarori 19 a Gombe

Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta buƙaci gwamnatin jihar ta bayyana ƙa’idojin da ta bi wajen naɗa sabbin manyan sakatarori 19, tana zargin cewa an yi watsi da wasu ma’aikatan gwamnati da suka shafe shekaru masu yawa suna aiki.

Sai dai jam’iyyar ta amince da ikon da Kundin Tsarin Mulki ya bai wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na naɗa Sakatarorin Dindindin, tana mai cewa ya kamata a gudanar da naɗin bisa gaskiya, cancanta da ƙa’idojin aikin gwamnati.

A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na PDP a jihar, Abdulqadir Ahmad Dukku, ya fitar, jam’iyyar ta yi zargin cewa wasu daga cikin sabbin manyan sakatarorin sun fito ne daga manyan makarantun gaba da sakandare da kuma wasu sassan ma’aikata da ba sa cikin tsarin aikin farar hula na jihar.

Sai dai PDP ta ce ba ta nufin cewa mutanen ba su cancanta ba, illa dai tana buƙatar gwamnati ta yi bayani kan matsayinsu na aiki, cancantarsu da kuma yadda suka shiga aikin gwamnatin jihar.

Jam’iyyar ta kuma sake duba batun naɗin daraktoci tara a matsayin masu kula da ma’aikatu — Overseer Permanent Secretaries (OPS) — da gwamnatin jihar ta yi a shekarar 2023.

A cewar PDP, matsayin OPS ba ya cikin tsarin aikin farar hula, don haka ya kamata a naɗa jami’an a matsayin Muƙaddashin Sakatarorin Dindindin, sannan a tabbatar da su bayan watanni shida ko kuma a mayar da su muƙamansu na daraktoci.

Jam’iyyar ta ce yayin da daga bisani aka tabbatar da wasu daga cikin jami’an da aka naɗa a matsayin masu kula da ma’aikatu, wasu kuma suka yi ritaya a matsayin daraktoci duk da cewa sun daɗe suna riƙe da mukaman.

PDP ta buƙaci gwamnatin jihar ta bayyana a fili ƙa’idojin da ta yi amfani da su wajen zaɓar manyan sakatarorin 19, tare da tabbatar da cewa an bi dokokin aikin gwamnati da ƙa’idojin hidimar farar hula na jihar.

Haka kuma, ta yi kira ga gwamnatin da ta sake duba duk wani naɗi da aka samu sahihin bayani da ke nuna wariya, son zuciya, cin karo da ƙa’idojin aiki ko kuma rashin bin ƙa’ida.

Jam’iyyar ta jaddada cewa matakin nata ba ya nufin yi wa sabbin sakatarorin bi ta da ƙulli, sai dai don nuna damuwa kan sahihanci da amincin tsarin naɗin.

Ta ce cancanta, ƙwarewa, gogewa, mutunci da nagartaccen aiki su ne ya kamata su zama ginshiƙan ci gaban ma’aikata da naɗin manyan mukamai a gwamnatin jihar, ba alaƙar siyasa ko son zuciya ba.

Comments (0)
Add Comment