Rayuwata A Hannun ’Yan Bindiga — Mai Shari’a Bunza

Rayuwata a hannun ’yan bindiga — Mai Shari’a Bunza

Bayan shafe kwanaki tara a hannun masu garkuwa da mutane, Mai Shari’a Faruk Hassan Bunza na Babbar Kotun Jihar Kebbi ya samu ’yancinsa. Bayan an sake shi, wakilinmu ta ziyarce shi a gidansa da ke Unguwar Chaki, Bunza, domin jin yadda ya kasance a lokacin da yake hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.

Ko da yake ya je an duba lafiyarsa bayan an sake shi, Mai Shari’a Bunza, wanda har yanzu ake iya ganin alamun gajiyawar da ya samu a daji, ya tarɓi wakilin namu hannu bibbiyu.

An sace Mai Shari’a Bunza daga gidansa da tsakar daren Asabar, 26 ga Yuli, 2026, sannan ya samu ’yanci a ranar Litinin, 3 ga Agusta, bayan shafe kusan kwanaki tara.

A baya, mun ruwaito wasu rahotanni da ke cewa ’yan uwansa cewa sun ce an biya Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa kafin a sako shi.

Wasu mutane biyar ɗauke da makamai ne suka kutsa gidan alƙalin da misalin ƙarfe 12 na dare, inda suka yi ta harbi sama domin tsoratar da mazauna yankin, sannan suka tafi da shi. Ba a samu asarar rai ko jikkata wani ba a yayin farmakin.

Washegari, Lahadi, masu garkuwar sun tuntubi iyalan alƙalin tare da neman Naira miliyan 200 a matsayin fansa. Bayan tattaunawa, an rage kuɗin zuwa Naira miliyan 50.

A ranar Litinin, 3 ga Agusta, aka samu labarin cewa an biya kuɗin fansan, inda masu garkuwar suka bar Mai Shari’a Bunza a kan wani tsauni kafin su bar sansaninsu.

Yadda aka yi garkuwa da shi
Da yake ba da labarin abin da ya faru, Mai Shari’a Bunza ya ce an kai shi wani wuri mai suna Dutsen Bandan, kusan kilomita 49 daga garinsu na Bunza.

Ya ce wurin yana kan wani tsauni a bayan sansanin dindindin na NYSC da ke Dakin Gari, Ƙaramar Hukumar Suru ta Jihar Kebbi.

Wani mazaunin Bunza, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Dutsen Bandan sanannen maɓoyar ’yan bindiga ne, kuma mazauna yankin sun daɗe suna korafin ganin mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne suna yawo a wajen.

Mai Shari’a Bunza ya ce lokacin da ’yan bindigar biyar suka shiga gidansa suka umarce shi da ya bi su, bai yi musu gardama ba.

A cewarsa, sun fita ta gefen gabas na gidansa, suka bi wata hanya da ke bayan gidaje, sannan suka nufi arewa zuwa wani ƙaramin wurin ban ruwa.

Daga nan suka juya yamma zuwa babbar hanya, suka ƙetare ta sannan suka nufi wani tsauni da ke yammacin garin Bunza.

Ya ce bayan sun isa tsaunin, suka nufi kudu zuwa hanyar Bunza-Kamba, suka sake ƙetare hanya sannan suka ci gaba da tafiya.

“Na yi tafiyar kusan kilomita 25 ba takalmi kafin mu isa Mahaɗar Tungar Bandan, inda suka bar baburansu domin gudun kada a gano su. Daga nan muka hau babura muka yi tafiyar kusan kilomita 24 kafin mu isa Dutsen Bandan, babban sansaninsu,” in ji shi.

Ya ce a jimlace, an tsare shi kusan kilomita 49 daga iyalansa na tsawon kwanaki tara.

Mai Shari’a Bunza ya ce yana zargin masu garkuwar sun daɗe suna bibiyar sa, inda ya yi imanin cewa suna da wasu ’yan leƙen asiri da ke ba su bayanai game da shi.

Rayuwa a sansanin ’yan bindiga
Mai Shari’a Bunza ya ce bai ga ’yan bindiga fiye da 20 a sansanin ba.

Ya ce an umarce shi da ya hau tsaunin bayan ya yi doguwar tafiya ba takalmi, lamarin da ya ce ya yi masa matuƙar wahala.

A saman tsaunin, ya tarar da wasu Fulani biyu da su ma aka yi garkuwa da su.

Ya ce ’yan bindiga biyar ne ke tsaron waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin da sauran ’yan bindigar suke zaune tare da iyalansu a ƙasan tsaunin.

Washegari, masu garkuwar sun nuna masa hotonsa da kuma na Shugaban Ƙaramar Hukumar Bugudu ta Jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi.

Sun tambaye shi ko mutumin da ke hoton shi ne, sannan suka ce an umarce su da su yi garkuwa da su duka, amma ba su bayyana wanda ya ba su umarnin ba.

Sun kuma nuna masa wani rahoton jarida kan sace shi, inda suka ce sun ji Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a biya Naira miliyan 200 domin a sake shi, amma wani mutum ya hana biyan kuɗin.

Bunza ya ce hakan ya nuna cewa masu garkuwar suna bibiyar labarai da abubuwan da ake wallafawa a kafafen sada zumunta.

“Masu garkuwar ba su azabtar da ni ba”
Mai Shari’a Bunza ya ce abin mamaki shi ne masu garkuwar ba su azabtar da shi ba a tsawon kwanaki tara.

“Sun kasance masu sauƙin mu’amala da ni. Ba su taɓa wulaƙanta ni ba. Abubuwan da suka fi damu na su ne hawan tsaunin da kuma doguwar tafiyar,” in ji shi.

Ya ce a duk lokacin da zai ci abinci ana rufe masa fuska domin kada ya ga fuskokin masu garkuwar.

Ya ce an tambaye shi irin abincin da yake so, inda ya zaɓi tuwon shinkafa ko semo da miyar kuɓewa.

A cewarsa, ana ba shi abinci sau biyu a rana tare da ruwan kwalba da lemon Maltina.

“Duk lokacin da suka kawo min abinci, sai su ce in ci har na ƙoshi. Idan ban gama ba, sai su ce kada in ji kunya, domin an kawo abincin ne domin in ci,” in ji shi.

Sai dai ya ce sauran mutanen Fulani biyu da aka yi garkuwa da su ba a ba su irin wannan kulawar ba. Ya ce idan sun nemi ruwa, ana ba su ruwan tafi mara tsafta.

Me ya sa aka sace shi?
Mai Shari’a Bunza ya ce yana ganin akwai manyan dalilai biyu da suka sa aka yi garkuwa da shi.

Na farko, kasancewarsa alƙali da ke yanke hukunci kan manyan laifuka, ciki har da shari’o’in ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Na biyu kuma, ya ce masu garkuwar sun samu labarin cewa shi attajiri ne da ke da motoci biyar, gidaje da gonaki da dama.

“Daga hirar da na yi da su, na fahimci cewa manufarsu ita ce kuɗin fansa. Ba su da niyyar kashe ni. Abin da suke nema shi ne kuɗi,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta kare alƙalai
Mai Shari’a Bunza ya nuna damuwa kan rashin isasshen tsaro ga alƙalai, musamman a gidajensu.

Ya ce lokacin da yake matsayin Majistate da Babban Majistate, yana da jami’an tsaro a gidansa, amma yanzu tsaron da ake ba su na wucin gadi ne.

Ya ce saboda yanayin aikinsu, alƙalai na cikin haɗarin kai musu hari, musamman saboda hukuncin da suke yanke wa’yan bindiga da masu aikata laifuka.

Ya yi kira ga gwamnati da ta samar wa alƙalai gidajen zama masu ingantaccen tsaro, tare da tabbatar da cewa kowane alƙali yana da jami’an tsaro a gidansa, musamman da dare.

Yadda ya samu ’yanci
Mai Shari’a Bunza ya ce Fulani biyu da aka yi garkuwa da su tare da shi sun tsere a ranar Asabar, 1 ga Agusta.

Ya ce bayan an karɓi Naira miliyan 50 na fansa a ranar Litinin, 3 ga Agusta, mafi yawan ’yan bindigar sun bar sansanin, suka bar mutum biyu suna tsaron sa.

Bunza ya ce daga baya ya ji ɗaya daga cikinsu yana cewa a harbe shi, amma ba a harbe shi ba.

“Daga ƙarshe sun bar ni suka gudu. Da misalin ƙarfe 5 zuwa 6 na yamma, na fahimci cewa babu kowa tare da ni. Sai na cire abin da aka rufe fuskata da shi, na sauko daga tsaunin,” in ji shi.

Ya ce ya ci gaba da tafiya har zuwa wani ƙauye da dare, amma ya ji tsoron shiga saboda yana zargin mai yiwuwa ’yan bindiga ne ke zaune a wurin, don haka ya ɓuya har zuwa safe.

Da safe ya ci gaba da tafiya har ya isa Kwanar Bandan, inda ya haɗu da wasu mazauna yankin.

Ya nemi babur da zai kai shi Bunza. Wani ɗan achaba ya ce zai kai shi kan Naira 8,000, amma daga baya wata motar Toyota Corolla mai gilashi mai duhu ta zo, inda direban ya amince ya kai shi kan Naira 2,000.

Sai dai a mahadar Ɗakingari ya sayi itacen girki na Naira 3,000 domin ya samu hujjar roƙon direban ya kai shi kai tsaye gidansa. Daga ƙarshe suka amince da Naira 3,000.

“Lokacin da na isa gida, na tarar da ’yan uwa da masu jaje a waje. Saboda gilashin motar mai duhu ne, babu wanda ya gane ni har sai da na fito daga motar. Sai mutane suka fara murna, kuma masu jajantawa suka ci gaba da tururuwa zuwa gidana,” in ji shi.

“Ba abin da zai sauya aikina a matsayin alƙali”
Da aka tambaye shi ko abin da ya faru zai shafi aikinsa, Mai Shari’a Bunza ya ce babu abin da zai sa ya ja da baya daga aikinsa.

“Wallahi, babu wani abu a duniya da zai sauya halina da jajircewata wajen gudanar da aikina na alƙali. Ina kan rantsuwa, don haka babu abin da zai sa na sauya ra’ayina wajen sauke nauyin da ke kaina,” in ji shi.

Ya ce abin da ya faru zai ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen gudanar da aikinsa.

Mai Shari’a Bunza ya kuma ce addu’o’in iyalansa, abokansa da sauran masu fatan alheri sun taka muhimmiyar rawa wajen samun ’yancinsa.

Ya ce mutane daga Bunza, Jihar Kebbi da ma sauran wurare sun yi masa addu’a sosai, kuma Allah Ya amsa addu’o’insu.

“Za a iya kawo ƙarshen garkuwa da mutane”
Mai Shari’a Bunza ya ce daga abin da ya gani, ’yan bindigar da suka tsare shi ba su da yawa, kuma jami’an tsaro za su iya fatattakar su idan aka ba su damar tunkarar su yadda ya kamata.

Ya kuma ce talauci da rashin ilimi na daga cikin abubuwan da ke ƙara jefa matasa cikin harkar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da ayyukan yi tare da inganta ilimi, ciki har da ilimin addinin Musulunci da na zamani.

Ya ce ya kamata gwamnati ta zuba jari sosai a fannin ilimi, ta samar da ayyukan yi ga matasa, sannan ta rage talauci.

A cewarsa, idan aka magance matsalolin talauci, rashin aikin yi da rashin ilimi, za a iya rage matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane sosai, ko ma a kawo ƙarshenta ɗungurungum.

Comments (0)
Add Comment