Shugaban jam’iyyar SDP na kasa ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya caccaki manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ka iya jefa shi cikin matsala a yunkurinsa na sake tsayawa takara a 2027.

Gabam ya lissafa cire tallafin mai ba tare da tanadi ba, daidaita kudin musaya, karin farashin wutar lantarki da na sadarwa a matsayin matakan da suka fi jefa al’umma cikin kunci.

Ya bukaci Tinubu da ya sake duba wadannan tsare-tsare tare da canza ministocinsa don ceto gwamnatinsa daga faduwa.

A cewarsa, irin gangamin da ake yi a yanzu yana kama da wanda aka yi a kan Jonathan a shekarar 2012, wanda ya hana shi sake cin zabe.  

Comments (0)
Add Comment