Abubuwa na cigaba da sauyawa a siyasar kasar nan, musamman a baya-bayan nan da aka samu yawaitar ƴan siyasa da ke ficewa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Jigo a babbar jam’iyyar hamayyar ta PDP, Sule Lamido, ya yi gargadin cewa ƙoƙarin rusa jam’iyyar tamkar yunƙurin murƙushe dimokaradiyya ne.
Sule Lamido wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne kuma tsohon ministan harkokin waje, ya ce ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC mai mulki tuggun ne da ba zai yi wa ‘yan siyasa daɗi ba nan gaba.
A ranar Litinin Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada Ifeanyi Okowa suka koma jam’iyyar APC a hukumance bayan sun bar PDP.
A baya-bayan nan wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa na Labour da NNPP sun koma APC ɗin, yayin da ake raɗe-raɗin wasu gwamnonin na kan hanyar komawa APC ɗin.