Trump Ya Sanya Harajin Kashi 15% Kan Najeriya da Wasu Kasashen Afirka

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya haraji na kashi 15 cikin dari kan kayayyakin da ake shigo da su daga Najeriya da wasu kasashen Afirka. Wannan mataki yana cikin kokarinsa na kare masana’antun cikin gida na Amurka da kuma dakile yawan kayayyakin da ke shigowa daga kasashen waje.

Rahotanni sun bayyana cewa harajin zai shafi kayayyaki da dama da Najeriya da sauran kasashen Afirka ke fitarwa zuwa Amurka, lamarin da ke barazana ga cinikayya da tattalin arzikin nahiyar.

Masana sun bayyana damuwa kan yadda wannan haraji zai iya rage yawan fitar da kaya daga Najeriya da kuma kara matsin lamba kan ‘yan kasuwa da masana’antu na cikin gida.

Comments (0)
Add Comment