’Yan bindiga sun jagoranci Sallar Juma’a a Sakkwato
’Yan bindiga sun harbe wasu mutum biyu har lahira tare da jagorantar sallar Juma’a a Babban Masallacin Izalah da ke ƙauyen Kaya a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato.
Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Juma’ar da ta gabata, inda suka shafe kusan sa’o’i bakwai suna cin karensu babu babbaka, ba tare da fuskantar wata turjiya ba.
Ya ce maharan sun tilasta wa mazauna ƙauyen zama a cikin gidajensu, yayin da su kuma suka riƙa shiga gida-gida suna satar shanu.
“Sun zo kauyenmu da misalin ƙarfe 11 na safe, suka ci gaba da ta’addancinsu har zuwa ƙarfe 5 na yamma. Suka tarwatsa mu, muka gudu zuwa cikin gidajenmu, amma suka ci gaba da shiga gidaje suna kwashe shanu. Ko sun ga mutane a cikin gidajen, ba ruwansu,” in ji mazaunin.
A cewarsa, da lokacin sallar Juma’a ya yi, ’yan bindigar sun nufi Masallacin Izalah, inda suka yi kiran sallah tare da jagorantar sallar.
Ya ce mafi yawan mazauna garin ba su je masallacin ba, inda suka ci gaba da zama a cikin gidajensu a lokacin sallar. Sai dai wasu kaɗan ne suka halarci sallar, kuma mafi yawansu yara ne.
Bayan kammala sallar, ’yan bindigar sun riƙa shiga shaguna, suka sace kayayyaki tare da kai wa masu sana’ar POS hari, inda suka kwashe kuɗaɗe har na miliyoyin Naira.
Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa shi ne wani mai POS mai suna Saidu Rabiu, wanda aka ce ’yan bindigar sun ƙwace masa sama da Naira miliyan shida a tsabar kuɗi, sannan suka tura Naira 500,000 daga asusunsa tare da ƙwace wayarsa.
Shaidan namu ya ƙara da cewa maharan sun kashe wasu mutane biyu, waɗanda ya ce sunayensu Maijega Sarkin Baka da Umar.
Ya ce Maijega Sarkin Baka shi ne shugaban mafarauta a yankin, kuma ’yan bindigar sun kashe shi ne bayan sun same shi a gonarsa.
Mazaunin ya kuma ce an tilasta wa wani mutum mai suna Mubarak Umar ya riƙa kora shanun da ’yan bindigar suka sace zuwa cikin daji, kuma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto bai dawo gida ba.
Ya ce maharan sun kwashe sama da shanu 500 daga ƙauyen a yayin farmakin.
A cewarsa, ’yan bindigar sun bar ƙauyen da misalin ƙarfe 5 na yamma, amma suka sake dawowa safiyar Asabar, suka ƙara kwashe wasu shanu, lamarin da ya bar mazauna kauyen cikin fargaba da rashin tabbas.
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su kawo musu ɗauki tare da ƙara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.