Rundunar ‘yan sandan Jihar Gombe ta bayyana cewa, ta kashe ‘yan bindiga uku tare da ceto mutane biyu a ƙauyen Lambo da ke yankin Pindiga a Karamar Hukumar Akko.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ya ce rundunar ta samu rahoton hare-hare da ake zargin ‘yan bindiga sun kai a ƙauyukan Rahama, Lambo da Garin Galadima da ke yankin Pindiga.
A cewarsa, da misalin ƙarfe 2 na rana ranar Asabar, ‘yan bindigar sun shiga ƙauyen Rahama ta hanyar Gagarabami, inda suka kashe wani dattijo mai shekaru 70, Tela Ahmadu, tare da sace ‘ya’yansa biyu.
Daga bisani da misalin ƙarfe 3:40 na rana, maharan sun kai hari ƙauyen Lambo, inda suka sace Babayo Garba, Malam Abba Musa da wani matashi mai shekaru 20, Baayo Bayi.
Rundunar ta ce Baayo Bayi ya rasa ransa, yayin da aka samu nasarar kubutar da Babayo Garba da Malam Abba Musa tare da kashe ‘yan bindiga uku.
‘Yan sanda sun kwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 68, mujallu huɗu, babura huɗu da gawarwakin ‘yan bindigar da aka kashe, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.