Sashen bada horo da jagoranci dake ofishin shugaban ma’aikata na jihar Jigawa yace a gobe Asabar 10 ga wata ne za a kai matasan jihar Jigawa zuwa makarantar horas da kananan hafsoshin soji ta NDA dake Kaduna domin ganawa dasu.
- Gwamnatin Jigawa zata cigaba da tallafawa Jami’ar Fasaha ta gwamnatin tarayya dake garin Babura
- Aƙalla mutum 42 ne suka mutu sakamakon ƙyanda a jihar Adamawa
- Gwamnan Jihar Gombe ya yi kira ga sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomi da su yi aiki tukuru
- Gwamna Dikko Radda ya kare ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai kasar Amurka
- Kasar Turkiyya ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra’ila
A sanarwar da Daraktan sashen Ibrahim Abdullahi ya bayar ta bukaci matasan da za a gana da su da su hallara a ofishin hukumar bada guraben karatu ta jiha dake Dutse da misalin karfe 7 na safe domin dibarsu zuwa Kaduna.
Sanarwar ta bukaci matasan da abin ya shafa da su kiyaye da wannan sanarwa kuma su zo akan lokaci.