Sashen bada horo da jagoranci dake ofishin shugaban ma’aikata na jihar Jigawa yace a gobe Asabar 10 ga wata ne za a kai matasan jihar Jigawa zuwa makarantar horas da kananan hafsoshin soji ta NDA dake Kaduna domin ganawa dasu.

A sanarwar da Daraktan sashen Ibrahim Abdullahi ya bayar ta bukaci matasan da za a gana da su da su hallara a ofishin hukumar bada guraben karatu ta jiha dake Dutse da misalin karfe 7 na safe domin dibarsu zuwa Kaduna.

Sanarwar ta bukaci matasan da abin ya shafa da su kiyaye da wannan sanarwa kuma su zo akan lokaci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: