Gidauniyar Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari da hadin gwiwar sashin kasafin kudi da tsara tattalin arziki na jihar Jigawa sun shirya taron masu ruwa da tsaki na yini daya kan ingancin abinci mai gina jiki a Dutse.

Da take jawabin bude taron wakiliyar gidauniyar, Dakta Fatima Jibrilla ta ce an shirya taron ne domin shigo da gwamnati da yan majalisar dokoki domin bunkasa aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu da ta kananan yara da kuma kara kasafin kudi domin cigaban da ake bukata.

Dakta Fatima Jibrilla ta ce haka kuma taron zai gano matsalolin da ake fuskanta na samar da kudaden aiwatar da shirin da nufin shawo kan lamarin

A nasa jawabin, daraktan hukumar lafiya matakin farko na jihar Jigawa, Dakta Shehu Sambo wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta, Malam Magaji Uba Ahmad, ya ce gwamnatin jihar Jigawa na bada miliyoyin naira a kowace shekara domin sayen gaydar tamuwa, yayin da kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar jigawa ke tallafawa shirin a kananan hukumomin su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: