Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna yace bangaren shari’a a jihar bazai sake bayar da belin masu fyade ba, daidai lokacin da ake duba yiwuwar dandake wadanda aka yankewa hukuncin fyade.
El-Rufa’i ya sanar da haka lokacin da wata tawagar mata da ke neman adalchi ga wadanda ake yiwa fyade, ta shirya wata zanga-zangar lumana a gidan gwamnati dake Kaduna a jiya.
Yace alkalin alakai na jihar ya bayar da tabbacin cewa daga yanzu baza a sake bayar da belin duk wanda aka zarga da aikata fyade ba, ta kowane hali, kasancewar suna komawa su sake aikata laifin.
- Sarki Charles zai koma aiki makon gobe
- Amurka ta bayar da bayanin tallafin soji na $6Bn da ta bai wa Ukriane
- Japan za ta taimakawa ƙananan ma’aikata a Najeriya domin samar da shinkafa
- Gwamnatin Jigawa ta jadadda kudirinta na daukar kwararan matakai na rage talauci a jihar
- An kama haramtattun nakiyoyi 6,240 a hanyar Yauri zuwa Jega da ke Jihar Kebbi
A cewarsa, tuni jihar take da tsatstsauran hukunci akan laifin aikata fyade.
Sai dai, El-Rufa’i yace gwamnati na duba yiwuwar gyaran dokar domin sanya dandaka ga duk wanda aka zartarwa da hukuncin fyade.
A cewarsa, tuni wani dan majalisar dokokin jihar ya shirya gabatar da kudiri akan sanya dandaka.