Rashin Malamai Ya Hana Yara Zuwa Makaranta A Abuja

Yaran makarantar firamare a ƙauyen Dogon-Ruwa da ke yankin Gawu, Karamar Hukumar Abaji a Babban Birnin Tarayya, sun daina zuwa makaranta sakamakon rashin malamai, in ji shugaban ƙauyen, Alhaji Sani Adamu.

Alhaji Adamu ya shaida wa manema labarai a fadarsa cewa, malamai da aka tura makarantar firamaren LEA ta ƙauyen sun daina zuwa aiki, lamarin da ya tilasta wa yara zama a gida ba tare da karatu ba.

Ya ce matsalar ta ƙara taɓarɓarewa ne bayan rahotannin hare-haren ‘yan bindiga a ƙauyukan makwabta kusan shekara guda da ta wuce, lamarin da ya sa malamai suka daina zuwa yankin.

Shugaban ƙauyen ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin fadar, dattawan al’umma da shugabannin ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) suka yi na neman mafita, ba a samu wani martani mai kyau daga hukumomi ko malamai ba.

Ya ƙara da cewa, ko da yake tsaron yankin ya inganta sama da shekara guda da ta wuce, malamai sun ƙi komawa makarantar, lamarin da ya sa iyaye suka fara amfani da ‘ya’yansu wajen ayyukan noma.

Alhaji Adamu ya nuna damuwa kan yadda makarantar ta lalace, inda ya ce wasu gine-ginen sun lalace, rufin ɗakuna ya tashi, rufin sama ya rushe, sakamakon rashin amfani da makarantar tsawon lokaci.

Don magance matsalar, shugaban ƙauyen ya buƙaci Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta FCT (UBEB) da ta ɗauki ‘yan asalin yankin da ke da shaidar NCE, tare da kuma roƙon gwamnati ta samar da rijiyoyin burtsatse na zamani domin magance matsalar ƙarancin ruwan sha da ke addabar al’ummar ƙauyen.

Comments (0)
Add Comment