Sojojin Najeriya Sun Kubutar Da Mutane 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kogi

Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane shida da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kogi, bayan wani hadin gwiwar samame a dazukan Ejiba da Saminaka.

Brigade ta 12 da ke Lokoja ta tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa daga Ag. PRO, Hassan Abdullahi, inda ta ce nasarar ta biyo bayan matsin lamba ta sama da kasa, tare da taimakon ‘yan sanda.

Daga cikin wadanda aka kubutar, biyar an riga an mika su ga iyalansu a Egbe da Ejiba, yayin da mutum na shida ke karbar kulawar likitoci saboda halin da yake ciki lokacin ceto.

Rundunar ta ce dakarunta za su ci gaba da sintiri a dazuka da maboyar miyagu domin karya duk wata barazana ga tsaron jihar.

Comments (0)
Add Comment