Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ba zai bari ’yan adawa su razanar da shi ba, yana mai kiran su masu hayaniya da ba sa mutunta doka da tsarin mulki.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata ganawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki na ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors daga jihohi 36 na ƙasar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Taron ya samu jagorancin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne babban daraktan ƙungiyar.
A yayin jawabinsa, shugaban ƙasar ya ce yunƙurin tsoratar da shi ba zai yi tasiri ba, yana mai jaddada cewa ya saba da irin waɗannan ƙalubale tun a baya.
“Shin suna son su tsoratar da ni ne? Wannan ƙarya ce. Na riga na saba da irin wannan haniyar,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar da cewa ba zai kauce daga gudanar da harkokin ƙasa ba, yana mai cewa zai ci gaba da mai da hankali kan shugabanci da ci gaban ƙasa.
Tinubu ya tuna da wahalhalun da ya fuskanta a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da kuma babban zaɓen 2023, inda ya ce duk da ƙalubalen da ya fuskanta, ya samu nasara.
Ya ƙara da cewa ƙwarewar da ya samu a harkar siyasa ta shirya shi domin fuskantar duk wani ƙalubale, kuma ba zai bari su karkatar da hankalinsa ba.
Shugaban ƙasar ya kuma jaddada muhimmancin bin doka da oda, yana mai cewa dole ne a mutunta umarnin kotuna ko da kuwa sun yi daidai da ra’ayin mutum ko akasin haka.
Ya ce: “Ba za mu amince da karya dokokin kotu ba. Dole ne mu mutunta ɓangaren shari’a, domin wannan shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya.”
A ƙarshe, Tinubu ya yi kira da a haɗa kai domin gina ƙasa mai cike da ci gaba da wadata, yana mai cewa hakan ne ginshiƙin manufar Renewed Hope.