Tinubu ya kori manyan jami’an da ya gada daga tsohuwar gwamnatin data gabata

Shugaban kasa  Bola Ahmad Tinubu ya kori shugaban Hukumar sanya idanu akan hada-hadar kasuwanci ta Najeriya FCCPC, Mista Babatunde Irukera da Darakta-Janar kuma shugaban hukumar BPE (Bureau of Public Enterprises), Alexander Ayoola Okoh.

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa an umurci shugabannin da aka kora da su mika ragamar aikin su ga  manyan jami’ai a hukumominsu, har sai an nada sabbin shugabannin zartarwa.

Fadar shugaban kasar ta ce bisa wannan umarnin na shugaban kasa, tsige su daga mukamansu ya fara aiki nan take.

Comments (0)
Add Comment