Amurka za ta binciki zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya ranar Alhamis

A ranar Alhamis, 20 ga Nuwamba 2025, Majalisar Wakilan Amurka za ta yi zama na musamman don bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.

Kwamitin Majalisar kan Harkokin Afirka ne ya saka wannan rana, domin duba matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashe masu sa ido na musamman (CPC), bisa zargin ana cuzguna wa Kiristoci.

Zaman dai za a gudanar da shi da misalin karfe 11:00 na safe a ɗaki mai lamba 2172 na Ginin Ofishin Rayburn, karkashin jagorancin Chris Smith (R-NJ). Za a kuma watsa shi kai tsaye ta intanet.

Shaidu da za su gabatar da bayani

Za a gabatar da manyan jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, da shugabannin addinai daga Nijeriya, ciki har da:

  • Jonathan Pratt, Babban Jami’in Ofishin Harkokin Afirka
  • Jacob McGee, Mataimakin Sakatare a Ofishin ’Yancin Dan Adam da Dimokuradiyya
  • Ms Nina Shea, Daraktar Cibiyar ’Yancin Addini
  • Bishop Wilfred Anagbe, Makurdi Catholic Diocese
  • Ms Oge Onubogu, Cibiyar Dabaru da Nazarin Ƙasashen Duniya

Abubuwan za a tattaunawa, majalisar za ta sake duba:

  • Zargin cin zarafin ’yan wani addini a Nijeriya
  • Matakan manufofi da Amurka za ta iya ɗauka
  • Takunkumi, taimakon jinƙai, da haɗin gwiwa da hukumomin Nijeriya
  • Hanyoyin dakile tashin hankali a yankuna dabam-dabam

Haka kuma, Sanata Ted Cruz zai gabatar da wani ƙuduri a Majalisar Dattawan Amurka kan wannan batu.

Comments (0)
Add Comment