Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan wani zama da ta yi da wakilan Gwamnatin Tarayya.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu.
Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa.
Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki.
Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin daɗin aikinsu.
Aminiya ta ruwaito yadda yajin aikin ya janyo ya haifar da tsaiko ga ayyukan lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sun fara yajin ne bayan ƙarewar wa’adin kwana 15 da ƙungiyarsu ta bai wa Gwamnatin Tarayya.
A ranar Asabar ne ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan wani taro ta Intanet da shugabanninta suka gudanar.
A ranar Juma’a, ƙungiyar ta gana da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar Ƙwadago, Ofishin Shugaban Ma’aikata, Ofishin Akanta-Janar, da Hukumar Albashi da Alawus da wasu ɓangarori na masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatunsu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, NANNM ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan duba yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.
Sanarwar, ta ce gwamnati ta ɗauki matakai masu muhimmanci kuma ta bayar da jadawalin lokacin da za ta cika alƙawuran.
Saboda wannan yarjejeniya da kuma samun masalaha, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin nan take.
Ta kuma umarci dukkanin ma’aikatan jinya da su koma bakin aiki, tare da gargaɗin cewa ba za ta amince a hukunta kowa ba saboda shiga yajin aikin.
Ƙungiyar ta gode wa mambobinta bisa goyon baya da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare haƙƙinsu.