Rikicin shugabancin jam’iyyar ADC ya kara tsananta

Rikicin shugabanci a jam’iyyar ADC ya kara kamari, bayan da wani ɓangare na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya gudanar da zanga-zanga a hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ke Abuja, suna neman a ba su sahalewar doka kan shugabancin jam’iyyar.

Zanga-zangar wadda aka gudanar a ranar Alhamis, ta samu jagorancin tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar, Nafiu Bala Gombe, tare da ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Kogi, Leke Abejide, da kuma daruruwan magoya bayan jam’iyyar.

Masu zanga-zangar sun zargi ɓangaren tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, da ƙoƙarin kwace shugabancin jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da suka ce ya saɓa wa tsarin dimokuraɗiyya.

Da yake jawabi ga jami’an INEC, Nafiu Gombe ya jaddada cewa dole ne a bi doka wajen warware rikicin shugabanci, yana mai cewa jam’iyyar ADC ba za ta amince da duk wani yunƙuri na karɓe iko ta hanyar da ba ta dace ba.

“Ba za a shigo jam’iyya ta baya a ce za a kifar da shugabanci ba. Wannan jam’iyya ta kowa ce daga matakin ƙasa har zuwa matakin unguwa,” in ji shi.

Shi ma ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya buƙaci INEC da ta ƙi amincewa da duk wani yunƙuri da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, yana mai cewa tsarin ya tanadi cewa dole ne mutum ya shafe aƙalla shekaru biyu a jam’iyyar kafin ya nemi wani babban matsayi.

A nasa ɓangaren, Daraktan Matasa na jam’iyyar, Mohammed Sahad, ya yaba wa INEC bisa bin umarnin kotu, tare da kira ga hukumar da ta tabbatar da Nafiu Gombe a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan INEC na Ƙasa, Abdullahi Abdu Zuru, ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa hukumar za ta duba korafe-korafensu tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.

Wannan zanga-zanga ta biyo bayan wata irin ta daban da ɓangaren Sanata David Mark ya gudanar a Abuja a ƙarƙashin taken # OccupyINEC, inda su ma suka zargi hukumar da take hakkin dimokuraɗiyya da kuma katsalandan a harkokin cikin gida na jam’iyyar.

Ci gaba da zanga-zangar daga ɓangarori daban-daban na nuna yadda rikicin shugabanci ke ƙara zurfi a jam’iyyar ADC, lamarin da ke haifar da damuwa kan makomar jam’iyyar a siyasar Najeriya.

Comments (0)
Add Comment