SHUGABAN KASA TINUBU YA YANKE HUTUN DA YAJE KASASHEN FARANSA DA BIRTANIYA, ZAI DAWO ABUJA A YAU TALATA

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kammala hutun aikinsa kafin lokacin da aka tsara kuma zai dawo Abuja a yau Talata 16 ga Satumba, 2025, domin ci gaba da aikinsa. 

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar a yammacin jiya Litinin, shugaban ya tafi kasar Faransa ne a ranar 4 ga watan Satumba, 2025, domin gudanar da wani ɓangare na hutunsa na shekara, kuma da farko an shirya yin hutun a tsakanin kasashen Faransa da Birtaniya.

A makon da ya gabata a birnin Paris, shugaba Tinubu ya yi wata liyafar cin abinci ta sirri da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, a fadar Elysée. 

Shugabannin biyu sun yi nazari kan muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Faransa, inda suka amince da zurfafa hadin gwiwa don samun ci gaban juna da kwanciyar hankali a duniya.

Manema labarai sun ruwaito cewa ba a bayar da wani dalili na sauya wannan hutu na shugaban kasar  ba.

Comments (0)
Add Comment