Hedikwatar Tsaro ta kasa ta sanar da cewa kimanin Yan bindiga 200 ne suka mutu, biyo bayan barin wutar da Rundunarsu da Operation Hadarin Daji suka kaddamar ta sama a maboyarsu na Jihohin Katsina da Zamfara, a yakin Arewa Maso Yamma.
Shugaban Sashen Yada Labarai na hukumar Major Janar John Enenche, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.
Inda ya ce Dakarunsu sun kashe Yan Bindigar ne a maboyarsu ta Ibrahim Mai’Bai cikin karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, da kuma kyauyen Kurmin Kura cikin karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Haka kuma ya ce sun kaddamar da harin ne bayan samun bayanan sirri wanda ya ce nuni da cewa Yan bindigar suna kokarin kaddamar da hare-hare ne akan wasu Yankunan da suke karkashin kananan hukumomi.