Hedikwatar Tsaro ta kasa ta sanar da cewa kimanin Yan bindiga 200 ne suka mutu, biyo bayan barin wutar da Rundunarsu da Operation Hadarin Daji suka kaddamar ta sama a maboyarsu na Jihohin Katsina da Zamfara, a yakin Arewa Maso Yamma.
Shugaban Sashen Yada Labarai na hukumar Major Janar John Enenche, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

Inda ya ce Dakarunsu sun kashe Yan Bindigar ne a maboyarsu ta Ibrahim Mai’Bai cikin karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, da kuma kyauyen Kurmin Kura cikin karamar hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
- An miƙa wa hukumar INEC ƙorafin yi wa Sanata Natasha kiranye
- An kama masu zanga-zanga 1,133 a Turkiyya cikin kwana biyar
- Ba lallai ba ne haɗakar ƴan siyasar Najeriya ta yi tasiri – Shekarau
- Fursunoni 12 sun tsere daga gidan yari a jihar Kogi
- An kama mutum 12 bisa zargin kashe wani matashi a masallaci a jihar Kaduna
Haka kuma ya ce sun kaddamar da harin ne bayan samun bayanan sirri wanda ya ce nuni da cewa Yan bindigar suna kokarin kaddamar da hare-hare ne akan wasu Yankunan da suke karkashin kananan hukumomi.