Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya saki fursunoni 293 wanda suke tsare a gidajen gyaran Da’a a jihar ta Kano.
Sakin nasu yazo ne bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta bawa Jihohi, kan su rage Cunkoso a gidajen gyaran da’ar, saboda annobar Coronavirus.
- An samu rahoton aukuwar gobara 271 tare da ceto rayuka 11 a Abuja
- An tsamo gawar mutane aƙalla 141 da kwale-kwale ya kife da su a jihar Neja
- Harin da Iran ta kai wa Isra’ila ‘ɗan ƙaramin hukunci ne’ – Khamenei
- Ƙungiyar Inter Miami ta lashe MLS Shield na ƙasar Amurka
- An sanar da ranar da za a gudanar da zaben Kananan Hukumomi a jihar Nasarawa
Mai magana da yawun Rundunar hukumar Gyaran Da’ar na Jihar Kano DSC Musbahu Lawan Nassarawa, shine ya tabbatar da sakin Fursunonin cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.
DSC Lawan, ya bayyana cewa gwamnan Jihar ta Kano ya biya kudi kimanin Naira Miliyan 12 ga Fursunonin tare da basu naira dubu 5 domin suyi kudin Mota zuwa gida.
Kazalika ya bukaci Fursunonin da aka saka su kasance masu canza halaiyar su, saboda damar da aka basu na zama mutanen kirki.