Ministan noma da raya karkara Sabo Nanono, yace ma’aikatarsa zatayi aiki tare da babban bankin kasa CBN domin tallafawa manoma dake fadin kasar da bashi mara kudin ruwa.
Ya bayyana hakane yayin karbar rahoton bincike kan matakin ayyukan noma a damunar bana, a cewar wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar Ezeaja Ikemefuna ya fitar jiya a Abuja.
Yace manufar hakan itace rage tasirin annobar cutar corona da kuma ambaliyar ruwa da aka fuskanta musamman a jihohin Kebbi, Jigawa da Kano.
Ministan ya bukaci manoman da su dada kaimi a noman rani, domin cike gibin da annobar ta haifar.
- Akalla mutum 60 ne suka mutu yayin ambaliayar ruwan sama kamar da bakin kwarya a Afghanistan
- An raba kayayyakin agajin gaggawa ga mutanan da suka gamu da iftila’in gobara a karamar hukumar Jahun
- Karamar Hukumar Gwaram ta nanata kudirinta na hana hakar duk wani nau’in ma’adanai a yankin
- Akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 za su fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa
- Kungiyar kwadago na zargin jam’iyyar APC mai mulki da sanya ‘yan Najeriya cikin wahala