Ministan noma da raya karkara Sabo Nanono, yace ma’aikatarsa zatayi aiki tare da babban bankin kasa CBN domin tallafawa manoma dake fadin kasar da bashi mara kudin ruwa.
Ya bayyana hakane yayin karbar rahoton bincike kan matakin ayyukan noma a damunar bana, a cewar wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar Ezeaja Ikemefuna ya fitar jiya a Abuja.

Yace manufar hakan itace rage tasirin annobar cutar corona da kuma ambaliyar ruwa da aka fuskanta musamman a jihohin Kebbi, Jigawa da Kano.
Ministan ya bukaci manoman da su dada kaimi a noman rani, domin cike gibin da annobar ta haifar.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba