Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya gargadi gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi dangane da haramta tsarin karatun Almajiranci.
Malamin ya ayyana cewa Almajirai suna da ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba a kudin tsarin mulki.
Da yake jawabi a karshen taron ganawar malaman Tsangaya, Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci a kyale Almajirai su cigaba da karatunsu na Al’Qur’ani a karkashin malamansu.
- Majalisar dattawa za ta fara zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan batun sake duba albashin alkalai
- Gwamna Namadi ya kaddamar da rabon kayan makaranta ga dalibai 30,000 a jihar Jigawa
- Adadin wadanda sukayi rajistar katin dan kasa na NIN ya kai 107,338,044
- Idan matatar Dangote ta fara aiki Nijeriya ba za ta kara bukatar shigo da man fetur ba
- Rundunar sojin Najeriya ta kubutar da akalla mutane 386 daga dajin Sambisa
A cewarsa, hakane ya kamata saboda Almajirai kamar kowane dan Najeriya, suna da damar gudanar da addininsu da yancin zama duk inda suka ga dama a cikin kasa, kamar yadda aka tabbatar a kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.
Ya ayyana cewa malaman Tsangaya baza su lamunci a take musu hakki ba ta hanyar haramta tsarin Almajiranci, da kuma kwashe Almajirai daga gari zuwa wani gari.